Connect with us

Labarai

Shirye Mu ke Dan Kawata jihar Kano–Archt.Yusuf Zarewa

Published

on

IMG 20230808 WA0139

Daga Rabiu Sanusi

 

An bayyana yunkurin gwamnati jihar Kano wajen shirin inganta kawata jihar dan maida ta daya daga cikin birane masu kyau a fadin kasar nan.

 

Shugaban hukumar kawata birni na jihar Achit.usuf Danjuma Zarewa ne ya bayyana haka ga manema labarai sa’ilin da yake rangadin duba wasu guraren shakatawa da yakai ziyara a ranar litinin dinan dan inganta hadakar aikin da injiniya Abba Kabir Yusuf ya dora shi akai.

 

Babban Darakaktan yace kamar yadda gwamna Abba Kabir ya kudurta na maida jihar wata duniya da zata zama gaban kwatance ya sa ya zabe shi matsayin Shugaban wannan hukuma dan kawo sauyin da ake so a jihar Kano wajen kawa.

 

Zarewa ya cigaba da cewa aikin wannan hukuma bawai ya tsaya a kawa bane kawai,akwai batun tsara sa talla ta allon da ake kafewa da duba tsaftar guraren shakatawa da sauran abinda ya jibanci kawo nishadi ga al’ummar jihar Kano baki daya.

 

Shugaban Hukumar yakuma bukaci dukkan masu gurin shakatawa da pack dasu zo dan cigaba da hada kai da gwamnati wajen ganin an taimaka a cigaba da haskaka jihar kano da wajajen shakatawa.

 

“Muna kuma Kira da babbar murya ga masu kula da wadannan guraren dasu kokarta zuwa dan biyan gwamnati kudin shiga dan cigaba samama masu ababen more rayuwa.”

 

Shima da yake jawabi Alhaji Hassan Isah wanda keda gurin shakatawa na saman kofar ruwa a Kan titin Katsina Roa, yace suna godiya matuka wajen yadda Gwamnati jihar Kano ke basu goyon baya wajen gudanar da aikin su.

 

Alh,Hassan yace ganin a Kano babu gurin shakatawa da yayi shura yasa suka assasa wannan sabon gurin shakatawa da nan bada jimawa ba zasu kammala.

 

Wadan su daga cikin guraren da shugaban ya ziyarta sun hadar da Big Brother suya spot,Fine Time, Junkies Nasarawa park,7:30,Chikinza, Piccadilly, Plate 2.

 

Sauran sun hada da Kano Garden, Kakuri Garden,Ali and Sultan park, Coffee and More Makbanes, Gemu Mai nama, Fanam Mai nama da dai sauran su.

 

Cikin wadanda suka rufama Shugaban hukumar baya yayin ziyarar aikin sun hada da daraktocin hukumar da sauran ma’aikata da manema labarai.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *