Connect with us

Labarai

Southampton ta rikito daga gasar Firimiyar Ingila

Published

on

VZ7PQCJVRJNZDBYAFGLPV5CSCE

Kungiyar Southampton ta fice daga gasar Firimiyar Ingila bayan da ta sha kashi da kwallaye 2-0 a wasan da ta kara da kungiyar Fulham a daren Asabar din nan.

Wannan rashin nasara da Southampton ta yi na nufin cewa ta koma gasar kwallon kafa mai daraja ta biyu a kasar Ingila, wadda ake kira da Championship a turance.

A halin yanzu kungiyar ce ta karshe a teburin gasar Firimiya da maki 24 duk da cewar da akwai sauran wasanni 2 da za a buga kafin karkare kakar wasa ta bana.

Karo na farko kenan cikin shekaru 11 da Southampton ke rikito wa daga gasar Firimiyar Ingila zuwa gasar Championship mai daraja ta biyu.

Kungiyar ta tsinci kanta cikin tsaka mai wuya ne bayan gaza samun nasara a wasanni 11 da ta bugajere da juna a bayan bayan nan.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *