Connect with us

Labarai

TJ & GP,DAG da TinT sun shirya taron Masu ruwa da tsaki kan harkokin haraji a Kano

Published

on

IMG 20231104 WA0089

Daga Rabiu Sanusi

 

Kungiyar bibiyar karbar haraji da aiki ga al’umma ta jihar Kano da kungiyar wanzar da zaman Lafiya da dorewar domukuradiyya hadin gwuiwar Follow Taxes sun shirya taron Masu ruwa da tsaki dan tattauna hanyoyin da yakamata abin wajen bunkasa harkar haraji a jihar Kano.

Taron dai nada nufin hada karfi da karfe wajen ganin an samu sahihiyar hanyar da zata taimaka wajen magance matsalolin da ake fuskanta a bangarorin tattara haraji a jihar Kano da take mataki na biyu wajen harkokin Kasuwanci a fadin Kasar nan.

A jawabin sa Abdul Ladan Ajumawa da yake darakta a ma’aikatar Kasafin kudi da tanadi ta jihar yace a yanayin da ake ciki yanzu wannan gwamnati tana da kuduri wajen ganin harkokin haraji sun bunkasa a matakin jiha.

Ajumawa yace babu wanda ya isa ya kalubalanci gwamnati kan haraji har sai yana biyan haraji,sannan kuma yace ta harajin ne gwamnati take da damar yima al’ummar ta aiki akoda yaushe.

Sai da daraktan ya ce hakkin gwamnati ne ta samar da mutane masu sanin yakamata tare da ilimi wajen karbar haraji ta yadda za’a samu kyakkyawar alaka da masu bada harajin.

” Kuma gwamnati ta kokarta wajen yima al’umma aiki da abinda suke biya,madamar gwamnati bazata bada kyakkyawar kulawaba ga al’ummar ta idan sun biya to babu wata hanya da za’a samu cigaba.”

Shima a nasa jawabin babban jami’in gudanar da shirye-shirye na DAG Sadiq Muhammad Mustapha ya yaba da irin goyon baya da kokari da Jama’a ke badawa a duk lokacin da aka bukaci su halarci irin wannan taro.

Sadiq Mustapha ya kara da cewa taron nada nufin samun hadin Kai na tsakanin masu biyan haraji da Yan kasuwa a kungiyan ce tare da masu ruwa da tsaki da gabatar da irin abubuwan da ke akwai a bangarori da fadakar da masu biyan haraji tare da Samar da hanyoyin bunkasa shi.

Haka Kuma ya bayyana irin kokarin da suke wajen gudanar da taruruka da masu da tsaki wajen wayar da Kai tare da hada masu ruwa da tsaki da kungoyi masu zaman kan su dan jin matsaloli da hanyar magance su.

Taron wanda DAG, Follow Taxes,Tax Justice and Government platform da IBP suka shirya a dakin taro na Tahir Guests Palace a karamar mulkin Nasarawa ta jihar Kano ya samu tallafi ne daga Christian Aid da IBP.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *