Connect with us

Labarai

Ukraine/Russia: EU na neman karin iskar Gas daga Najeriya

Published

on

download

Kungiiyar Tarayyar Turai (EU) na kokarin yaukaka dangantaka da Najeriya domin samun karin wuraren da za ta sayi iskar gas da nufin rage dogaro ga Rasha.

Najeriya ce kasa ta hudu da ke safarar iskar gas zuwa Turai, inda aka yi kiyasin cewa kusan kashi 40 cikin 100 na gas din da kasar ke fitarwa ana kai shi kasashen Turai ne.

Tarayyar Turai na son dakatar da sayen gas daga Rasha a matsayin martani kan yakin da ta kaddamar a Ukraine.

Jami’an diflomasiyyar Turai sun ziyarci Najeriya a ranar Litinin, inda suka gana da shugabannin kamfanin mai na NNPC.

“Matsayinmu ba wai ya tsaya na babbar abokiyar huldar Najeriya ba, muna son kulla alaka da kasar ta fannin mai da iskar gas, saboda yawancin kamfanonin da ke aiki tare da ku na kasashen Turai ne. Mu ma muna son zama daya daga cikin abokan huldarku,” in ji jakadan Tarayyar Turai a Najeriya Samuela Isopi.

Shugaban kamfanin mai na Najeriya NNPC sun tabbatar wa wakilan Turai cewa a shirye kamfanin yake ya kara yawan gas din da yake fitarwa a kasuwannin duniya.

Hukumomin Najeriya sun ce kasar ta tabbatar tana da iskar gas da ta kai yawan cubic tiriliyan 209.5 a watan Junairun shekarar 2022.

Yayin da kasar ke samun kashi biyu na kudaden shigar da ake tarawa gwamnatin Najeriya

 

BBC Hausa

1 Comment

1 Comment

  1. Mo

    April 12, 2022 at 9:44 pm

    Kungiyar banzayen arewa dai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *