Labarai
Yadda Ta Ke Wakana a Gasar Kwallon Kafa Ta Zakarun Turai.

Daga Ibrahim Halliru Muhàmmad
Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta kasar Sifaniya zata Kara da Manchester city ta kasar Ingila a gasar Kwallon Kafa Ta zakarun Turai a zakaye na kusa da karshe. Real Madrid ta doke kungiyar kwallon kafa ta Chelsea har gida da ci 3-1 a filin wasa na Stamford Bridge, sannan daga bisani a filin wasa na Santiago Barnabue Chelsea ce ta samu nasara akan Real Madrid din da ci 3-2. Wanda hakan ya bawa kungiyar Real Madrid dama ta zuwa zagaye na gaba da banbancin kwallayen da suka zurawa Chelsea har 5-4.
A wani bangaren Kuma kungiyar kwallon kafa ta Liver pool ta kasar Ingila zata kece raini da Villarreal. Bayan da Liver pool ta samu nasara akan takwarar ta Benfica dake a kasar potugal a zagaye na farko da ci 3-1 a filin wasa na Estàdio da Luz a birnin Lisbon. A zagaye na biyu kuwa canjaras aka tashi Liver pool nada 3 Benfica ma nada 3 a filin wasa na Anfield. Hakan ya bawa Liver pool damar zuwa zagaye na kusa da karshe.
Ita kuwa Villarreal ta doke Bayern Munich ne a filin wasan ta na Estàdio de la ceramica na kasar Sifaniya. Yayin da Kuma suka yi kunnan doki a filin wasa na Allianz Arena dake birnin Munich.
Wasannin zasu zo ne ranakun 26 da 27 na watan Aprilu da muke ciki a zagayen farko, sannan Kuma zagaye na biyu a rana kun 3 da 4 na watan mayu Mai kamawa.