Connect with us

Labarai

Yakin Sudan ya shiga mako na 6

Published

on

BQLFOZXDMJIJ7GFA652IMWFJAA scaled

Jiragen yaki sun cigaba da luguden wuta kan wasu yankuna da ke wajen Khartoum babban birnin Sudan daga daren ranar Juma’a zuwa wayewar garin Asabar.

Shaidun gani da ido sun ce, baya ga Khartoum, jiragen yakin sun yi ruwan bama bamai a kudancin Omdurman da kuma arewacin Bahri, biranen da kogin Nilu y araba da babban birnin kasar ta Sudan.

Shaidun da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito, sun kara da cewar a cikin birnin Khartoum dai kura ta lafa, koda yake ana iya jiyo sautin harbin bindigogi lokaci zuwa lokaci.

A halin da ake ciki, kazamin fadan da ake gawbzawa tsakanin sojojin gwamnati na shugaba Abdel Fattah al-Burhan da dakarun RSF masu biyayya ga tsohon mataimakinsa Hamdan Daglo, ya shiga mako na 6.

Dubun dubatar fararen hula ne dai fadan ya rutsa da su a kasar ta Sudan, kuma lamarin ya fi muni a birnin Khartoum, inda matsalar rashin abinci, ruwan sha da sauran kayayyakin bukata ke karuwa, biyo bayan yadda dakarun soji da ke fafatawa juna suke fasa manyan shaguna da gidaje, laifin da bangarorin biyu ke musanta aikatawa.

Ya zuwa yanzu dai kididdiga ta nuna cewar fiye da mutane miliyan 1 suka zama ‘yan gudun hijira, yayin da wasu akalla dubu 1 ko sama da haka suka rasa rayukansu, yayin da dubu 5,287 suka jikka, tun bayan barkewar fadan na Sudan a ranar 15 ga watan Afrilun da ya gabata.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *