Labarai
Yan bindiga sun kashe kusan mutun dubu 3 cikin wata uku–Rahoto

Wani rahotan binciken da aka gudanar a Najeriya yace mutane 2,968 Yan bindiga suka kashe a Jihohin Neja da Kaduna da Zamfara a cikin watanni 3, yayin da akayi garkuwa da wasu 1,484.
Binciken da kungiyar sanya ido akan harkokin tsaron Najeriya ta gudanar da ake kira ‘Nigeria Security Tracker’ yace mutanen da ake kashewa a yankin Arewa Maso Yamma ya zarce wanda akeyi a kowanne sashe.
Rahotan binciken yace ‘Yankin Arewa ta tsakiya itace ta biyu wajen kashe kashen, inda tayi asarar mutane 984, sai kuma Arewa maso Gabas wadda tayi asarar mutane 488.
A yankin kudu maso gabas inda ake fama da masu fafutukar kafa kasar Biafra, an hallaka mutane 181 a wadannan watanni, yayin da aka kashe mutane 127 a Kudu maso Yamma da 85 a Kudu maso Kudu.
‘Yan bindigar da aka bayyana a matsayin ‘Yan ta’adda na ci gaba da kai munanan hare hare Yankin Arewa maso Yammacin Najeriya inda suke hallaka mutane tun daga shekarar 2017.
Wadannan mahara sun kashe mazauna karkara da kwashe dukiyoyin su da kuma garkuwa da wasu daga cikin su domin karbar fansa, yayin da manoma da matafiya ma basu tsira ba daga hare haren wadannan mutane.
Yayin da Yan bindigar ke hallaka jama’a a Arewa maso Yamma, mayakan boko haram na ci gaba da kai hare hare a yankin Arewa maso Gabas.
RFI Hausa