Connect with us

Labarai

‘Yan ta’adda sun kashe sojojin Nijar 6 a kusa da iyakar Burkina Faso

Published

on

Sojojin Jamhuriyar Nijar

‘Yan ta’adda sun kashe sojojin Nijar 6 a wani hari da suka kai a kudu maso yammacin kasar, a wani yanki da ke kan iyaka da kasar Burkina Faso.

Cikin sanarwar da ta fitar, ma’aikatar tsaron Jamhuriyar Nijar ta ce wasu gungun ‘yan ta’addan sun yi wa wata tawagar sojoji da ke rakiya ne kwantan bauna a gundumar Kolmane, bayanin farko kan harin na ranar Alhamis da ma’aikatar tsaron ta fitar.

Sai dai ba a tantance hasarar da aka yi a bangaren maharan ba.

Harin ta’addancin dai shi ne na biyu cikin kwanaki goma a yankin Tillaberi bayan shafe makwanni ana kwanciyar hankali.

Tillaberi, yanki ne mai fadin gaske da ke kan iyakokin kasashen Burkina Faso da Mali, wanda ya sha fuskantar munanan hare-haren zubar da jini daga kungiyoyin ‘yan ta’adda masu ikirarin jihadi da ke kawance da Al-Qaeda da kuma kungiyar IS tun shekara ta 2017.

A makon da ya gabata wasu ‘yan ta’adda suka kai hari kan wata motar bas da wata babbar mota a yankin na kudu maso yammacin kasar ta Nijar, inda suka kashe akalla mutane 21.

 

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *