Connect with us

Labarai

Yau Litiniin Buhari zai kaddamar da matatar man Dangote

Published

on

images 3 2

A yau Litinin ake sa ran shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da sabuwar matatar man kamfanin Dangote da aka gina a Lagos, wanda ake sa ran ya rika tace gangar mai dubu 650 kowacce rana domin rage wahalar shigar da tacaccen mai cikin kasar

Ana sa ran wannan matata ta rika tace man fetur da man dizil da kalanzir da kuma man jiragen sama, matakin da ake ganin zai rage matsalolin da ake fuskanta yanzu na rashin samun wadataccen man da ake tacewa a cikin gida.

Bayanai sun ce a makwanni masu zuwa ake saran kamfanin ya fara aiki gadan gadan a matatar wadda ita ce mafi girma da wani ‘dan kasuwa ya mallaka a nahiyar Afirka, kuma wadda ake sa ran ta samar da kasuwar da ta kai Dala biliyan 21 kowacce shekara wajen sayan danyan mai daga hannun gwamnatin Najeriya.

Shirin kaddamar da kamfaninya haifar da matukar farin ciki tsakanin jami’an gwamnati mai barin gado da masu harkar mai da iskar gas da kuma ‘yan Najeriya da dama saboda ci gaban da kamfanin zai samar ta bangaren kasuwanci da kuma ayyukan yi.

Har ila yau kaddamar da kamfanin na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriya ke kokarin kawo karshen tallafin da take zubawa a bangaren man fetur domin ganin jama’ar kasar sun sayi man a cikin rahusa.

Alkaluma sun nuna cewar tallafin da gwamnati ke zubawa domin sayar da man da arha a cikin gida ya tashi daga naira miliyan 351 a shekarar 2005 zuwa naira triliyan 4 da biliyan 390 a shekarar 2022.

A wannan shekara kawai gwamnati ta kasafta kashe naira triliyan 3 da rabi a matsayin kudin tallafin na watanni 6 kawai.

Shugaban kamfanin Dangote, Aliko Dangote ya ce matatar za ta taimaka wajen taskance Dala biliyan 10 na kudaden kasashen ketare da Najeriya ke amfani da shi wajen sayo tacaccen mai da kuma samar da Dala biliyan 10 daga cikin wanda za’a sayar wa kasashen ketare.

Akalla shugabannin kasashe 5 ake sa ran su halarci bikin kaddamar da matatar.

RFI HAUSA.

 

 

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *