Connect with us

Labarai

Yunwa ta tagayyara mutane fiye da miliyan 43 a kasashen Afirka 3

Published

on

KKRWDIJK4VJWLCB5CBG2IN6CYM scaled

Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane fiye miliyan 43 ne a kasashen Habasha, Somalia da Kenya ke cikin tsananin bukatar agajin gaggawa domin ceto su daga tagayyara har ma da rasa rayuka.

Hukumar da ke kula da ayyukan jin kai a majalisar ta dinkin duniya OCHA ta ce, kusan mutane miliyan 24 daga cikin miliyan 43 da aka ambata, sun riga sun fada cikin bala’in yunwa a kasashen na Habasha, Kenya da kuma Somalia.

Kasashen uku dai a yanzu haka na fuskantar bala’in fari mafi muni cikin shekaru 40, lamarin da ya janyo rashin saukar ruwan sama a wasu yankunansu saboda tasirin matsalar sauyin yanayi.

Kididdiga dai ta nuna cewara kasar Somalia kadai, akalla mutane miliyan 6 da dubu 700 ke fama da karancin abinci, cikinsu kuma har da kananan yara fiye da dubu 500.

Wannan hali da aka shiga ya sa babban sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterres jagorantar taron kasashe a birnin New York da zummar tara dala biliyan 7 don tallafawa wadanda yunwar ta  tagayyyara a kasashen da ke yankin kuryar gabashin Afirka.

Sai dai kawo yanzu kashi 20 cikin 100 na adadin tallafin da majalisar dinkin duniya ta nema kawai  aka iya tarawa.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *