Connect with us

Labarai

Za mu ceto karamar hukumar Dala daga halin da take ciki==Hon Aminu Yaro

Published

on

IMG 20230823 WA0125

Dan takarar shugabancin karamar hukumar Dala karkashin jam’iyyar NNPP dake jihar Kano,Hon Aminu Mamman Yaro,ya bayyana kudurin sa na ceto karamar sa daga Mawuyacin halin da take ciki na rashin kula wajen ilimi musamman na primary.

Hon.Aminu Yaro ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai ranar talatar wannan makon.

Dan takarar yace karamar hukumar Dala da take gaba a daya daga cikin kananan Hukumomi 44 da ke jihar Kano wajen yawan jama’a ta tsinci kanta matakin koma baya musamman wajen harkokin ilimi da tsaro.

Sannan yakuma bada tabbacin cigaba da tallafama mata da matasa wajen harkokin dogaro dakai da bada jari domin dogaro dakai a wannan karamar hukumar ta Dala.

“A shirye muke wajen tabbatar da samar da kyakkyawan tsaro a wannan karamar hukuma tamu tare da nema ma matasan mu Maza da Mata hanyar da zasu dogara da Kan su ta hanyar da ta dace.”

Daga bangaren Mai girma gwamna Abba Kabir Yusuf kuwa dan Hon.Aminu Yaro yace a yanzu ne jihar Kano ta samu shugaba tun daga lokacin da Engr Rabiu Musa Kwankwaso ya jagoranci jihar matsayin gwamna.

Shugaban Kwankwassiya Duban yace ayukan da Abba Kabir Yusuf yafara cikin kankanin lokaci da suka hadar da maido da martabar Hasiya Bayero sa samar da fitilun Kan Titi tare da gyaran su na daga cikin Jajircewar gwamna na ciki alkawarin da yadaukar ma al’umma.

Bayan wadannan ayuka Kuma akwai Samar da ruwan Sha da tsaro da Mai girma gwamna yayi cikin kankanin lokaci tare da nada mataimaka da za su taimaka masa da sauran aikace-aikacen alkhairi da yake da niyyar yima al’ummar jihar kano.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *