Connect with us

Labarai

Zaben Sanata Hanga da Madakin Gini A Majalisa Ta Goma An Yi Shi Ne Bisa Cancanta-Hamisu Dogon Nama

Published

on

IMG 20230704 WA0166

Hon. Hamisu Sa’ad Dogon Nama wanda daya ne daga cikin jiga-jigan ‘yan jam’iyyar NNPP ne, na kasa, ya taya Sen. Rufai Sani Hanga murna bisa zaben shi da aka yi, a matsayin Mataimakin Marasa Rinjaye na mai tsawatarwa na majalisa ta goma (Deputy Minority Chief Whip ) a majalisar tarayya.

Sannan kuma ya kara taya Hon. Aliyu Sani Madakin Gini bisa zaben shi da aka yi, a matsayin Mataimakin Shugaban Marasa Rijaye (Deputy Minority Leader), a majalisar tarayya.

Dogon Nama ya yi wannan murnar ne, a lokacin da yake ganawa da ‘yan jarida, a babban birnin jihar Kano, a yau Talata 4 ga watan Yuli, 2023.

“Wannan zaben da aka yi, tabbas an yi shi ne bisa chan-chanta, duba da irin kwarewarsu akan abin da ya shafi sha’anin aikin majalisar Tarayya.

” Idan aka tuna a baya, anga irin gudunmuwar da Sen. Hanga da Madakin Gini suka bayar wajen kawo kudurori domin cigaban Jihar Kano har da kasa gaba daya,” inji Hamisu Dogon Nama.

Dogon Nama yaci gaba da cewa samun matsayin Sen. Rufai Sani Hanga tare da Aliyu Madakin Gini wani babban cigabane wanda ‘yan Kano zasu amfani domin kare martabar bangaren da suka fito, tare da bijiro da manyan aiyukan da mutane zasu amfana wanda ya shafi bangaren ilimi, lafiya, kasuwanci, samarwa matasa aikin yi, a mataki daban-daban da sauran su.

A kashe ya yi musu addu’ar Allah ya taimake su tare da sauran ‘yan majalisu.

✍🏼 *Hamisu Sa’ad Dogon Nama Media Team*

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *