Connect with us

Labarai

Kotun A Gombe Ta Mayar Da Filin Mechanic Village Da Aka Yi Takaddama A Kai Ga Emir General Integrated LTD

Published

on

Babbar Kotun Jihar Gombe, karkashin jagorancin Mai Shari’a Daurabo S. Sikkam, ta yanke hukunci a shari’a mai lamba GM/116/2026, inda ta tabbatar da cewa Kamfanin Emir General Integrated Ltd ne keda sahihiyar mallakar filin da ya kai hekta 1.30 a kan hanyar Gombe Bajoga, kusa da ofishin NURTW a cikin garin Gombe.

 

 

Wakilin mu ya ruwaitoh cewa wannan hukunci ya biyo bayan doguwar takaddama ta shari’a da aka yi tsakanin Emir General Integrated a daya bangaren da Grandscope Construction Ltd, Gwamnatin Jihar Gombe, Babban Lauyan Jihar Gombe, da kuma Kwamishinan Ayyuka, Gidaje da Sufuri.

 

 

 

A cikin hukuncinta, Mai Shari’a Sikkam, bayan ta ce ta yi nazari sosai a kan takardar kara da aka gabatar a kotu a ranar 30 ga Agusta, 2025 tare da hujjoji da bayanan lauyoyi daga bangarorin biyu, a cewarta bisa la’akari da bayanan da aka gabatar a kotu ta gamsu da cewar Takardar Mallakar Kasa mai lamba GM/15926 na mai kara har yanzu tana da inganci kuma tana da karfi sahihanci.

 

 

Kotun tace ayyukan gwamnati da jami’anta na bayar da kwangila ga Kamfanin Goundscope Construction Ltd, wanda ya haifar da rushewar gine-ginen mai kara da kuma gina abubuwa ba bisa ka’ida ba a cikin filin da ake takaddama, inda kotun ta bayyana irin wannan aiki a matsayin haramtacce da kuma take hakkin mallaka.

 

 

Kotun ta bayar da umarnin hanawa ta dindindin ga wadanda ake kara, wakilansu ko jami’ansu daga sake tsoma baki cikin mallakar filin na mai kara.

 

 

 

Mai Shari’a Sikkam kuma ta umurci waɗanda ake kara da su rushe duk ginin da sukayi a filin da kwashe komai da abubuwan da suka gina a cikin filin.

 

Bugu da kari, kotun ta bayar da diyya ta musamman ga Emir General Integrated Ltd har Naira miliyan 15 da kuma diyya ta gaba daya har Naira miliyan 50, tare da kuɗin shari’a da aka kididdige Naira 7,200.

 

 

Hukuncin ya kuma dora kaso 10 na riba a kowace shekara kan kudin da aka bayar har sai waɗanda ake kara sun biya cikakke.

 

 

Bayan hukuncin kotu lauya ga mai kara, Barrister Sulaiman Abdurrahim, ya bayyana wannan hukunci a matsayin nasarar adalci.

 

Ya jaddada cewa bisa dokar Land Use Act (LUA), idan gwamnati ta nemi mallakar filin da ke da amfani ga jama’a, dole ne ta sanar da mai filin tare da biyan diyya, musamman idan filin ya na da ingantattun takardun mallaka CoO “Wanda muka tsayawa yana da sahihan Takardun Mallaka amma gwamnati ta kasa bin ka’ida. Haka kuma ta yi watsi da umarnin kotu sau biyu da aka bayar a baya don dakatar da ci gaba da aiki a filin,” in ji shi.

 

 

Barrister Abdurrahim ya kara da kira ga Gwamnan Jihar Gombe, Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya, da ya yi biyayya ga hukuncin kotu ta hanyar biyan diyya na Naira miliyan 65 da aka yanke, tare da kwashe dukkan kayayyaki da gine-ginen da aka yi a filin.”

 

Ya jaddada cewa bin umarnin kotu ba kawai zai dawo da adalci ga Kamfanin da muka tsayawa ba, har ma zai tabbatar da bin doka da oda a Jihar Gombe.

 

A ranar da aka yanke hukunci, lauya ga Kamfanin Grandscope Construction, da lauyan da ke wakiltar Gwamnatin Jihar Gombe, Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje da kuma Babban Lauyan Gwamnatin Gombe ba su halarci zaman kotun ba.

 

 

Da yake magana da Wakilin Justice Watch Hausa wani mai nazarin shari’a, Auwal Isa ya ce: “Wannan hukunci ba wai kawai ya dawo da hakkin mallaka ga Emir General Integrated Ltd bane kawai, har ma ya aika da sako mai karfi kan take hakkin mallaka da ake samu ba bisa ka’ida.”

 

A cewar mai nazarin, hukuncin ya karfafa ingancin Takardar Mallakar Kasa (Certificate of Occupancy) tare da jaddada rawar da kotuna ke takawa wajen kare ‘yan kasa daga tsoma bakin gwamnati da kuma kamfanoni ba bisa doka ba.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending