Connect with us

Labarai

Jihar Gombe Ta Kaddamar Da Shirin Taimakawa Kananan Yan Kasuwa na Fadar Shugaban Kasa

Published

on

IMG 20240407 WA0063

Daga Abubakar Abdullahi Gombe

 

Gwamnatin jihar Gombe ta kaddamar da wani gagarumin shiri da nufin tallafawa masu kananan sana’o’i, kanana da matsakaitan masana’antu (MSMEs) ta hanyar fara tantance wadanda zasu ci gajiyan tallafin da Shugaban kasa ya bayar.

Shirin wanda ofishin Babban Mataimaki na Musamman ga Maigirma Gwamnan Jihar Gombe, Hon Abdulwahab Sabo ya jagoranta, shirin ya shafi sama da mutane dubu goma sha daya da suka amfana a fadin kananan hukumomin jihar goma Sha daya (11).

A karkashin wannan shirin, kowane wanda ya ci gajiyar shirin zai samu tallafin naira dubu hamsin, inda zai samar da tallafin kudi da ake bukata a yayin da ake fuskantar kalubalen tattalin arziki.

Har ila yau Hon. Abdulwahab Sabo ya mika godiyarsa ga shugaban kasa Ahmad Bola Tinubu da ma’aikatar kasuwanci da masana’antu bisa wannan dama da suka ba jihar Gombe.

Ya kuma yi kira ga al’ummar jihar Gombe da su ci gaba da marawa gwamnati mai ci baya, karkashin jagorancin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, shugaban kungiyar gwamnonin Arewa, a kokarinsu na bada romon Demokaradiyya ga Talakawan Jihar Gombe .

Ana shi Jawabin Malam Babangida Usman na bankin masana’antu wanda Yana daya daga cikin masu tantance mutanen ya yabawa gwamnatocin Jihohi da na tarayya bisa bullo da wannan shiri na rage radadin da talakawa ke ciki a wannan marrar.

Usman ya ce ana sa ran aikin tantance mutane sama da dubu goma sha daya zai dauki tsawon kwanaki tara.

Bugu da Kari wasu daga cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin da suka nuna jin dadinsu da tallafin sun hada da Yusuf Alhaji Ibrahim Ma’ajin kungiyar masu tuka Keke Napep da Harisa Muhammad daga Bye Pass Barunde a karamar hukumar Akko da Abdullahi Yakubu shugaban Yan’Balangu na jihar Gombe.

Sun yabawa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya da Shugaban kasa Ahmad Bola Tinubu kan yadda suka tallafa masu a dai dai lokacin da ake bukata a wannan lokaci na hanu baka hanu kwarya, inda suka yi alkawarin yin amfani da kudaden wajen bunkasa kasuwancinsu.

Ƙaddamar da PPP a Jihar Gombe ya nuna irin ƙoƙarin da gwamnati ke yi na ƙarfafa ƙungiyoyin MSME da haɓaka haɓakar tattalin arziki a matakin farko. Tare da masu cin gajiyar shirin yin amfani da waɗannan tallafin don haɓaka kasuwanci da dorewa, shirin yana da alƙawarin haɓaka kasuwanci da haɓaka ci gaban zamantakewa da tattalin arziki a faɗin jihar Gombe.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *