Connect with us

Labarai

Kungiyar Yan Chanji Ta WAPA A Kano Ta Yi Tsookaci Kan Karyewar Farashin Dala

Published

on

Screenshot 20240408 145244 1

Shugaban Kungiyar Masu hada-hadar kudaden canji ta kasashen waje dake jihar Kano, Alhaji Sani Dada ya bayyana jin dadinsa bisa yadda gwamnatin tarayya take kara karya farashin dala kowanne lokaci a kasar.

Alhaji Sani Dada ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da Manema labarai a ofishinsa dake kasuwar canji ta Wapa, Kano.

Yace rage farashin kudaden waje da babban bankin Kasa yayi, zai fitar da masu hada-hadar canji daga zarge zargen al’umma na cewa sune suke da alhakin tashin gwauran zabin da kayayyakin masarufi suke yi a Kasuwannin Nigeria.

Shugaban yace wannan kalubale na tsadar kayayyakin masarufi yanzu ya rage tsakanin yan kasuwa da al’ummar Kasar, saboda yanzu jama’a za su fahinci inda gizo yake saka.

” A baya Mutane sun zage mu mun dora mana alhakin tashin Dala Wanda kuma muma bamu da katabus a kai, amma saboda rashin fahimta mutane suka rika Kalubalantar mu har da dora mana alhakin tashin farashin Kayan masarufi”. Inji shi

Sani Dada yace kungiyar masu hada hadar canji ta Wapa, ta himmatu wajen ganin an kara inganta rayuwar matasa musamman, ‘ya’yan Kungiyar masu hada hadar canji domin rage marasa ayyukan yi da kuma farfado da tattalin arzikin Najeriya.

Daga karshe Shugaban ya bayyana cewa, Kungiyarsa a shirye take wajen baiwa Gwamnati cikakken hadin kai domin ciyar da jihar Kano da ma Kasa baki daya

Kadaura 24

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *