Labarai
Duniya ta gaza kare rayukan fararen hular da rikice-rikice suka rutsa da su – Guterres

Sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterres ya ce gwamnatoci da sauran hukumomi sun gaza wajen kare rayuka da dukiyar miliyoyin fararen hular da tashe-tashen hankula ko yaki suka rutsa da su.
Guterres ya koka ne da bayan da wata kididdiga ta nuna cewar an samu karuwar kashi 53 cikin 100, na adadin fararen hular da ke rasa rayukansu sakamakon yaki da sauran nau’ikan tashe-tashen hankula a fadin duniya cikin shekarar 2022.
Rahoton ya nuna cewar fararen huka kusan dubu 17 suka mutu a cikin tashe-tashen hankula har kashi 12 da suka barke a shekarar da ta gabata.
Sakataren majalisar dinkin duniya ya ce misali a bayyane yake kan yadda aka gaza kare rayukan fararen hula a Ukraine, Sudan, Habasha da kuma Syria, inda a nan ne matsalar tafi kamari.
Guterres ya kara da cewa alkaluman da suka tattara na nuni da cewar kashi 94 cikin 100 na adadin wadanda hare-haren bam suka halaka cikin shekarar bara a yankuna masu cinkoson jama fararen hula ne.
A kasar Ukraine kadai, wadda dakarunta ke gwabza yaki da takwarorinsu na Rasha yau sama da shekara guda, majalisar dinkkin duniya ta ce, fararen hula kusan dubu 8 ne suka mutu, yayin da wasu fiye da dubu 12 suka jikkata.